Posts

Maganin Korar Aljanu A Jikin Mutum

Image
  Maganin Korar Aljanu A Jikin Mutum Domin kawar da jinn da ke cikin mutum: Ana rubuta Suratul Ya-Sin kafa 1 a Allo. A duk lokacin da ka kai ga kalmar "Mubin, sai ka rubuta Suratul Al-Jinn kafa 1 kafin ka ci gaba da karatun Suratul Ya-Sin. Kaci gaba har ka kammala rubutun gaba ɗaya. Bayan ka gama, ka wanke rubutun da ruwa mai tsarki. Kowane dare, ka sha kaɗan daga ruwan sannan ka shafa a jikin ka gaba ɗaya. Ka ci gaba da yin haka na tsawon kwanaki 21. Ka guji yin jima’i ko wata hulɗar auratayya yayin wannan magani. Asararu Zallah Foundation 08109934185

Sirrin Bude Kofofin Arziki - Asararu Zallah

Image
  Sirrin Bude Kofofin Arziki - Asararu Zallah Yayana ko yayata, idan kana jin kamar an toshe maka hanyoyin samunka, yan sihiri suna damunka, ko komai ya tsaya ga abin da za ka yi: Ka samo tafarnuwa da gishirin girki, sannan ka ɗauko kwalba mai ruwa. Sai ka karanta wannan acikin kwalbar ruwan: (Hasbiyallahu la ilaha illa Huwa, alayhi tawakkaltu, wa Huwa Rabbul-Arshil-Aẓim) kafa 99. Bayan ka karanta, sai ka zuba gishiri a cikin ruwan, sannan ka murje tafarnuwar ka saka a ciki. Da wannan ruwan, kullum kana goge jikinka da safe kafin ka fita, sannan da yamma kafin ka kwanta bacci. Wallahi, wannan kun fayakun ne ka gwada, za ka ga yadda Allah zai sanya albarka a ciki.  Asararu Zallah Foundation  08109934185

Sirrin Gigitacciyar Mallaka - Asararu Zallah

Image
  Sirrin Gigitacciyar Mallaka - Asararu Zallah Barka da warhaka kowa da kowa, wannan sirrin soyayya ne, domin ka sa mutum ya ƙaunace ka. Idan saurayinki ko budurwarka ta ƙi sonka, kana iya yin wannan sirrin: Ka nemo goro fari, farin goro, sai ka rubuta sunan ka a gefe ɗaya, sannan a gefe ɗaya kuma ka rubuta sunan mutumin da kake so. Bayan haka ka buɗe goron daga ciki, sai ka saka allura kamar yadda kuke gani a hoto, sannan ka riƙa faɗa cikin niyyar ka cewa: “Ina soke zuciyar (ka ambaci sunansa ko sunanta)...” Yayin da kake yin haka, ka yi fatan soyayya yadda kake so dangantakarku ta kasance duk irin soyayyar da kake fata. Da zarar ka gama, sai ka ɗauki goron ka zuba masa turare Bint Sudan, ka yayyafa a jikin goron gaba ɗaya. Daga nan, ka kai goron zuwa gidan da (tururuwa) ke zama. Sannan ka yi gaisuwa da su kamar haka: “Assalamu alaikum gidan tururuwa, ya ku kakanni na wannan gida, na kawo muku aiki, ina roƙonku ku tura soyayya cikin zuciyar (ka ambaci sunan mutumin).” Wannan shine...

Sirrin Farin Jini Na Suratul Yusuf

Image
  Sirrin Farin Jini Na Suratul Yusuf Hatimin Suratul Yusuf, wata hanya ce mai karfi domin samun karɓuwa a ko’ina, khma sirrine mai kyau dake karawa mutum farin jini mai karfin gaske. Domin a kasance ana karɓarka a duk inda kake cikin iyalinka, wajen aiki, ko duk inda ka je, wannan sirri yana da tasiri sosai. Kamar yadda kowa ya san labarin Annabi Yūsuf (A.S.), yadda aka jefa shi cikin rijiya, sannan daga baya Allah Ya sa duk wanda ya ganshi yana ƙaunarsa, haka ma wannan asiri yake aiki, In shaa Allah. Ana rubuta wannan hatimin a takarda ranar Litinin, ko Alhamis, ko Jumma’a, ko Asabar, sannan a ba wanda yake bukata ya saka a jiki. In shaa Allah Ta’ala, wannan mutum zai kasance ana karɓarsa da ƙaunarsa a ko’ina ya shiga a jarraba  Ga hatimin nan: Asararu Zallah foundation 08109934185

Sirrin Farin Jini Mai Karfi - Asararu Zallah

Image
  Sirrin Farin Jini Mai Karfi - Asararu Zallah Asirin samun soyayyar mutane, mutun zai kasance ana ƙaunarshi, da samun manyan abokan ciniki musamman ga yan kasuwa... wannan yana daya daga cikin talisman na Suratul Fatiha kuma malamai dayawa sun san shi suna aiki dashi dari bisa dari. Kalmar asirin ita ce: أرسط مكصوه علقبد حتضنذغي 3005 (watau arsadan maksuhu alqabidu hataran zaghiyu). Wanda ya san asirin nan ko ince badinin wannan talisman zai iya samun duk abin da yake so. Zai kasance ana ƙaunarsa daga manyan mutane, shugabanni, kuma zai samu buɗaɗɗen alheri, har ya mallaki zukatan masu girman kai. Domin a ƙaunace ka kuma ka samu soyayyar mutane, ka riƙa yin zikri na wannan kalma sau 3005 da safe da yamma, ka fara ranar Alhamis, insha Allahu za'a ga biyan bukata. Asararu Zallah Foundation 08109934185

Sirrin Biyan Bashi Nan Take Mujarrabun

Image
  Sirrin Biyan Bashi Nan Take Mujarrabun. Ga waɗanda suke bashi yai musu yawa kuma ba sa iya biya, ma'ana Allah bai hore musu abunda zasu biya dashi ba to ga wani sirri da zasu iya jarrabawa insha Allahu za'a samu biyan bukata cikin kankanin lokaci. Ana rubuta wannan tauraron na ramli wanda ake kiranshi da naqiyyatul khaddi, shine tauraron gidan 14 a taurarin ramli, wannan tauraron ana rubutashi ne kafa 945. Ma'ana ana samun babban Allo sai a dinga rubuta wannan shakalin ai ta rubuta shi har sai an tabbata ya kai kafa 945 babu ragi ba kari, a kula idan aka rage aiki bazai yuwu ba, hakama idan aka kara aiki bazai yuwu ba saboda haka ayi rubutun da taka tsantan ko mai ya futo dai dai saboda samun cikar biyan bukata. Yadda ake amfani da shi: Wannan rubutun idan ka gama shi zaka samu ruwa mai tsarki mai tsabta sai ka wanke shi bayan ka wanke shi sai kake shafa shi a jikin ka safe da yamma na tsawon kwanaki 9, tare da yin addu’o’in bukatunka, ma'ana addu'oi akan Allah ya...

Sirrin Mallakar Rauhani Mai Saukin Gaske

Image
  Sirrin Mallakar Rauhani Mai Saukin Gaske Wannan Fa’idar sunan Allah "Ar-Rashīd" (الرشيد): Malamai na cewa wanda ya yi aiki da wannan sunan Allah, zai samu taimakon ruhani mai suna (Bughtiya’il), Mutum zai kasance ya shiga Halwa sannan kullum sai ya karanta sunan Allah (Ar-Rashid) kafa 16,000 a kowace rana da dare. A lokacin da ka fara gabatar wannan aiki, ana son mutum ya kasance: Ya daina cin duk abin da ke da rai (nama, kifi, kwai da sauransu), Kuma ya daina cin ko amfani da abin da ke fitowa daga halittun masu rai, Ya ci abinci halal, Kuma ya saka kaya na halal.  Ana cewa sai mutum ya killace kansa na tsawon wasu watanni, a cikin ɗaki mai tsabta (halwa), har sai ruhanin ya bayyana tare da aljanu bakwai masu imani kuma musulmai, da farko zasu gaishe shi, shi kuma ya amsa. Sai su ce masa: “Ya bawan Allah, me kake so?” Ya ce: “Neman yardar Ubangiji Mai Girma da kuma kasancewa tare da kai (ruhanin).” Sannan malamai sukace zai ba shi dutse fari (hajar abyadh), amma yanada sha...

Sirrin Bude Kofofin Arziki Da Warware Asiri

Image
  Sirrin Bude Kofofin Arziki Da Warware Asiri Sirrin “Surar Li'ilafi Quraish” domin buɗe hanyoyi kofofin arziki da aka rufewa mutum da kuma warware duk nau'in Asiri dake jikin mutum kai tsaye babu bata lokaci, da kuma yaye wasu kwararar damuwa, da kawar da abubuwan sharri a jiki. Ya kai ɗan’uwa, ya ɗan’uwana abinda ake cewa Akan sirrin surar “Li'ilafi” yana aiki ne wajen tsarkake jiki daga sharrin da ke ciki, kuma yana lalata duk wata kazantar makiya dake jikin mutum, sannan yana gaggawar rusa makiya duk karfin su kai ko wanene shi Allah zai yi maka maganin shi. amma sai ka gwada ka gani da kanka, saboda ba zan iya bayyana komai ba tukuna, dan wannan sirrin wallahi mun jarrabashi yafi sau a irga kuma munji dadin shi kada kuyi wasa dashi, mun bawa mutane da dama munyiwa mutane dayawa sunji dadin shi, kuma ku jarrabashi insha Allahu zaku ga dace shi. Yadda ake aikin: A rubuta “Surar Li'ilafi” Kafa 41 a wanke da ruwa mai kyau sannan sai a samu wake fari a dafa wannan wake ...

Sirrin Jalabi Mai Karfin Gaske - Asararu Zallah

Image
  Sirrin Jalabi Mai Karfin Gaske - Asararu Zallah A nemi ƙulli-ƙulli guda bakwai daga wannan tsiro mai suna Kantakara wasu suna kiranshi da jan ganye wasu Kuma taramniya sai a sa su cikin sabon tukunya, a saka ruwa, a bar su su jike a ciki tsawon kwanaki 7, sannan a yi wanka da wannan ruwan na tsawon kwana 7. Inji Malamina ya ce wannan aiki yana taimakawa wajen samun budi ne, wato domin a sami kuɗi, arziki, da ci gaba. Sannan fa Ana iya amfani da tushensa wajen yin wankan domin samun kariya daga sharrin aljanu a wasu al’adu. Asararu Zallah foundation  08109934185

Sirrin Samun Dukiya Da Rufin Asiri - Asararu Zallah

Image
  Sirrin Samun Dukiya Da Rufin Asiri - Asararu Zallah Ana samun ganyen gwandar daji guda 666 ko wanne Ana rubuta masa Wannan Tauraron ramlin mai suna Isqafi kafa 666. Sai a wanke wannan zanen, sannan a yi wanka da shi tsawon kwanaki 3 idan namiji ne, ko kwanaki 4 idan mace ce. A lokacin da ake yin wankan, ana hawa wani abu mai ɗan tsawo kamar dutsen ƙarami, ko kujerar da ke sama, ana yin hakan don nufin cewa mutum zai hau matsayi mai girma ko samun buɗewa. Wannan sirrin yanada girma sosai kada ayi wasa dashi, dan nasameshine daga daya daga cikin malaman kasar Senegal wanda yasha bani sirruka masu karfin gaske kuma tabbas idan na jarraba su ina ganin biyan bukata dai dai gwargwado Alhamdulillah. Saboda haka kuma ku rike shi zaku ga amfanun shi insha Allahu rabbi. Asararu Zallah foundation  08109934185

Sirrin Bude Manyan Alheri: Salatin 1813 ga Kashifu al-Ghumma

Image
  Sirrin Bude Manyan Alheri: Salatin 1813 ga Kashifu al-Ghumma 📖 Bayani Mai zurfi Ma’anar “كَاشِفُ الْغُمَّةِ”  “Kashif al-Ghumma” (كَاشِفُ الْغُمَّةِ) na nufin Mai cire damuwa ko Mai warware ƙunci (wato Allah ne wanda yake kawar da damuwa). Salatin “اللهم صل على كاشف الغمة” yana nufin “Ya Allah, ka yi salati (fatan rahama da salama) ga Mai Cire Damuwa” — wato an nufi Annabi Muhammad ﷺ a matsayin wanda addu’o’insa, albarkarsa, zasu taimaka wajen sassauta wahala da damuwa. Wurin wannan salati a cikin ibada:  Ana cewa a karanta wannan salati kafa 1813 da dare, bayan sallar Tahajjud (wato bayan farkawa da dare don yin ibada) ba tahujjud na ramadan ba, ana nufin sallar nafila da akeyi da daddare.  Ana maimaita wannan salati tsawon kwanaki 21, Wannan hanya ana ɗaukar ta a matsayin wata ibada mai karfi da ake sa ran Allah zai buɗe babban alheri, sassauta damuwa, ya kawo sauƙi da ƙarin rahama ga mai yin ta da zuciya da tawakkali.  Sharhin Ilmi da hankali.  Kamar ...

Sirrin Mallakar Mace Na Har Abada

Image
  Sirrin Mallakar Mace Na Har Abada Don riƙe mace har abada a gidanta , wato riƙe matar da take son barin mijinta da son ranta: A nemi kaza wadda take zaune a kan kwai nata kullum , wato lokacin da kaza ta kwanta tana ruga ƙwai, tana ci gaba da zama a kansu har sai sun fito. A wannan lokacin ne za a ɗauki wannan kaza, a wanke ƙafafunta biyu a cikin ruwa mai tsabta a cikin wani kwano. Sai ayi  addu’a a kan wannan ruwan, sannan a ba matar da take son barin gidanta ta sha wannan ruwa . Insha Allah, za ta daina son barin gidanta kuma za ta zauna har abada . Amma idan namiji ya yi amfani da wannan hanya don cutar da matarsa ko ya yi niyyar mugunta da ita , to zai sami tozali da cikas a rayuwarsa a kowane fanni,  babu abin da zai yi ya yi masa kyau. Asararu Zallah foundation 08109934185

Sirrin Samun Manyan Kudade Na Halal

Image
  Sirrin Samun Manyan Kudade Na Halal. Wannan sirrin: Sirrin Samun Manyan Kudade Na Halal tare da wannan sirri za ku zama 'yantattu wajen samun kuɗaɗen masu yawa, ana Rubuta Suratul Qari'ah kafa 102; amma bayan kowace ayah na surar, zaka rubuta sunan ka. A nemo Farin rago wanda babu digon baki a jikinsa, to da farko sai a raba rubutun gida biyu;  na farko a zubashi acikin abincin ragon da ruwan shansa sai a bashi yaci kuma yasha na tsawon kwana 12. Idan ragon ya mutu kafin cikar kwanaki 12, hakan na nufin aikinka ba zai yi aiki ba. Idan bai mutu ba kafin cikar kwanaki 12, ku yi murna bukata zata biya. A rana ta 12, bayan sallar asuba, sai yi addu'i sosai domin burinku ya cika, sannan a yanka wannan ragon. A raba dukkan naman zuwa sassa uku: daya tare da kai da kafafu A dauki kashi ɗaya a ajiye a gida, sauran a ba da a matsayin sadaka ga mutanen waje. Sauran  ruwan da ya rage, a saka a cikin farin roba, sai kuma a saka wuri guda 102 aciki, kuma sai a ajiye rubutun a w...

SIRRI AKAN KOWACE IRIN DAMUWA KO BUKATA

Image
  SIRRI AKAN KOWACE IRIN DAMUWA KO BUƘATA ‎ ‎Akoda yaushe ba'a taɓa raba mutum da damuwa in ma dai na kuɗi ko lafiya ko na halin zamantakewar rayuwa kowa da irin yadda Allah yake jarraba shi daga cikin Nau'o'i na damuwa kuma akoda yaushe ana fafutuka ne wajen ganin an samu waraka daga wannan damuwa muna fata Allah ya cigaba da yayemana damuwarmu baki ɗaya. ‎ ‎To kamar yadda muka faɗa in har kasan kana cikin wata damuwa kowacce iri ce ban rage maka ko guda ba kuma kake da burin ganin Allah ya ɗauke maka ita to ga wannan sirri ka jarraba shi ni dai fatana duk wanda yaga wannan sirri yayi ƙoƙarin yi don Allah don Annabi Muhammadu s.a.w wallahi wallahi babu kaffara acikin wannan rantsuwa in har Allah yabaka damar aiwatar da wannan to zaka samu kuɓuta daga cikin duk wata matsala ko damuwa sannan buƙatarka kowace iri ce Allah zai biya maka Insha'allahu. ‎ ‎Ga yadda zaka yi: ‎ ‎Zaka yi nafila raka'a huɗu kowacce raka'a Fatiha ɗaya Inna'anzalnahu ƙafa huɗu duk raka...

SIRRIN KORAR JUNNU AJIKIN MUTUM MUJARRABUN INSHA ALLAH

Image
  SIRRIN KORAR JUNNU AJIKIN MUTUM MUJARRABUN INSHA ALLAH  Ina Masu Fama Da Baqaqen Junnu Ko Nature Ko Masu Hana Aure Ko Masu Lalata Harkoki Ko Na Farfadiya.  To Kusamo Ganyen Tumfafiya Wanda yayi ja Yafado Gasa kokuma yayi ja Asaman iccen Tumfafiyar Ta Asamo ganyen guda 7 Sai Arubuta Ayatul kursiyu kafa 1 Akowane Ganyen Sai A shanyashi yabushe idan yabushe Adakashi tareda tafarnuwa.  Sai Aringa Yima Mai Wannan Matsalar hayaki da wannan maganin To Insha Allah zasu rabu Kosunaso Ko Basuso Zaisama Cikakkiyar Lafiya Daga Matsalar Junnu Harkokinka Zasu Dawo.  Kudaure Kuturama yan'uwa donsu Amfana Masha Allah Asararu Zallah foundation  08109934185

MAGANIN ULCER MUJARRABUN SAHIH

Image
  MAGANIN ULCER MUJARRABUN SAHIH YAN UWA GA WANI NA KAWO SHA MAGANIN ULCER NE, MUJARRABUN SAHIH, INSHA ALLAHU DUBA D YADDA YAN UWA SUKE FAMA DA MATSALAR ULCER SHI ASA NAGA DACEWAR NA KAWO.DOMIN MU FANA UBANGIJI YA HADA MU ALADAN BAKI DAYA, UBANGIJI YA INGANTA MANA LAFIYA BAKI DAYA, GA YADDA AKE AIKIN:-- ANA SAMUN BAWON LEMON ZAQI, SAI AWANKE SHI, SOSAI ADORA AWUTA A TAFASA SHI, ZA ADINGA SHANSA DA DUMINSA, DA SAFE DA YAMMA, INDAI MAGANAR MATSALAR ULCER CE, TO ANYI BAN KWANA DA ITA INSHA ALLAHU. IF YOU ARE HAVING ULCER PROBLEM HERE IS REMEDY FOR IT, FIRST OF ALL YOU SHOULD GET, AN ORANGE WHEN YOU TAKE IT, THE COVER OF IT, YOU SHOULD WASH IT WITH A CLEAN WATER, THEN BOIL IT, WITH A FRESH WATER, YOU SHOULD BE DRINKING IT, TWICE PER DAY, MORNING AND EVENING TIME, INSHA ALLAHU ALL YOUR ULCER PROBLEM WILL BE A HISTORY IT WILL BANISH AND GOD WILL HEAL YOU INSHA ALLAHU, THIS ASRAR IS TESTED AND TRUSTED Daga Mallam Ma'aruf Hayat Asararu Zallah foundation  08109934185

Sirrin Samun Arziki Da Dukiya Masu Yawa

Image
  Sirrin Samun Arziki Da Dukiya Masu Yawa Wannan sirrin: Sirrin Samun Arziki Da Dukiya Masu Yawa ياعمروش ياكندريوش ياطشلمشهشم WANNAN SIRRINE DA MANYAN MALAMAI KE BOYE SHI  Yana ɗaya daga cikin sirrikun danake amfani dasu shekaru da yawa,  Ana karanta wannan sunan ياعمروش ياكندريوش Ƙafa 1000 Sai wannan ياطشلمشهشم Shima ƙafa 1000 Ga wanda bazai iya karanta shi ba to ya duba jikin hoton nan akwai mai wasalin sa  Sai kuma a karanta wannan zajra na jikin fefan nan wanda ya fara daga allahuman nan Ƙafa uku ko 7 To wallahi in dai kana yin wannan aikin kaida talauci kun raba hanya, Allah zai buɗa maka ƙofofin samunka zai azirta ka ta hanyoyi da daban daban kuma zai mallaka maka zuciyoyin jama'a da zasu ke zuwa maka da abubuwan alkairai Daga ƙarshe mutane suna copy sirri suje suita bazashi ko ina sakaka Ni dai banyi wa wanda zai yi hakan ba izini, amma in dai zakayi amfani dashi dan ka ƙari kanka da iyalanka da yan uwanka to tabbas nai maka izinin, kada a maida shi na neman k...

Sirrin Sunan Allah Mai Karfin Gaske

Image
  Sirrin Sunan Allah Mai Karfin Gaske Wannan sirrin: Sirrin Sunan Allah Mai Karfin Gaske. NA RANTSE DA ALLAH, NA RANTSE DA ALLAH, NA RANTSE DA ALLAH Wannan sirrin kashafin sa akamun kuma yadda aka bani shi akace naje nayi bincike akan wa'yannan sunayen,  Allahu  Muhammadu Hakimu Amma sirrin la'ilaha illallahune Aka kuma bani satar amsa akace muzajansu zanyi Wallahi wallahi koda na farka na ɗauki takarda da biro nafi awa 1 ina nazari akan wannan ismin dan bazai yiwu ince kashafin nan karya bane sannan na rasa makama Na zauna nayi addu'a na kara dubawa koda na haɗa adadin su sai naga sun bani 236 sai nayi shiru nace ai wannan adadin KUMFAYAKUN ne  Koda na fara muzaja kamar haka ا ل ل ه م ح م د ح ك ي م Kunga in mukayi muzaja zai zama  امحلحكلميهمد Wato AMUHALHAKIN LAMAIHUMUDU sai na sake tunani shin ta ina yake da alaƙa da la'ilaha illallah wallahi da iriga adadin harrufan sai naga su goma sha biyu ne 12 kunga adadin Laila laha illallah ai 12 wallahi sai da naji ha...

Dafa'i Da Jalabi Mai Karfin Gaske

Image
  Dafa'i Da Jalabi Mai Karfin Gaske Yan uwa ahlullahi ina yiwa kowa fatan Alkairi da kuma fatan samun nasara a duk in muke. Sirrin: Dafa'i Da Jalabi Mai Karfin Gaske sirrine mai girma kuma yana daya daga cikin sirrukan da muke aiki dasu. Allahumma salli ala sayyadina Muhammadu Alfatihi lima ugliqa wal katimi lima sabaqa nasiril haqqi bil haqq wal hadi ila siradikal mustaqim wa'ala ahlihi haqqa qadrihi wa miqidarihil azim. Wannan sirrin sirrine na dafa'i kuma jalabi kuma ibɗali saboda hatimine na Alqur'ani mai girma kuma JAMIUL KULLI A rubuta shi asha a shafe jiki na tsawon kwana 7, son samu ace kullum ƙafa 7 kai ko ƙafa ɗaya ne yayi, insha Allahu za'a dace. Duk mai matsalar rashin jalabi zai iya jarraba shi, mai matsala rashin dafa'i ma zai iya aikatashi duk matsalar da kake dashi xaka iya aiki dashi kuma za'a ga biyan bukata insha Allahu. Ga hatimin nan: Asararu Zallah foundation 08109934185

DAFA'I MAI KARFI NA YANKAN SHAKKU

Image
  DAFA'I MAI KARFI NA YANKAN SHAKKU Wannan sirrin suna:  DAFA'I MAI KARFI NA YANKAN SHAKKU, dafa'i ne kuma kariya ne daga duk wani abun tsoro ko abun ki, wannan kuma kwarjini ne a idon makiya mai mayarwa kowa aniyarshi bi izinillahi ta'ala. Ranar Alhamis Kar a manta za'a rubuta wannan sirrin a sa'ar mushtari ma'ana karfe 6:30 na safe ko 1:30 na azahar ko 8:30 bayan isha ko 3:30 na dare za'a rubuta wannan hatimin kafa 7, hallau a wanke shi a sa'ar mushtari a saka kaikayi koma kan mashekiya aciki a sha a sa'ar mushtari sai kuma a rike wuridin li'ilafi ba adadi mallam baka bina bashin rantsuwa zakasha mamaki kwarai da gaske billahil wallahi Duk wanda ya jarraba wannan sirrin zaiyi alfahari damu kuma zaiji dadin yadda muke kokarin ganin mun taimakon da muke sakarwa, kuyi kokarin ganin kun turawa sauran yan uwa domin suma su amfana da wadannan sirrukan da muke sakewa kuma insha Allahu zamu kawo sirruka mabambanta domin amfanar daku masu bibiyar ...