Sirrin Bude Kofofin Arziki Da Warware Asiri
Sirrin Bude Kofofin Arziki Da Warware Asiri
Sirrin “Surar Li'ilafi Quraish” domin buɗe hanyoyi kofofin arziki da aka rufewa mutum da kuma warware duk nau'in Asiri dake jikin mutum kai tsaye babu bata lokaci, da kuma yaye wasu kwararar damuwa, da kawar da abubuwan sharri a jiki.
Ya kai ɗan’uwa, ya ɗan’uwana
abinda ake cewa Akan sirrin surar “Li'ilafi” yana aiki ne wajen tsarkake jiki daga sharrin da ke ciki, kuma yana lalata duk wata kazantar makiya dake jikin mutum, sannan yana gaggawar rusa makiya duk karfin su kai ko wanene shi Allah zai yi maka maganin shi.
amma sai ka gwada ka gani da kanka, saboda ba zan iya bayyana komai ba tukuna, dan wannan sirrin wallahi mun jarrabashi yafi sau a irga kuma munji dadin shi kada kuyi wasa dashi, mun bawa mutane da dama munyiwa mutane dayawa sunji dadin shi, kuma ku jarrabashi insha Allahu zaku ga dace shi.
Yadda ake aikin:
A rubuta “Surar Li'ilafi” Kafa 41 a wanke da ruwa mai kyau
sannan sai a samu wake fari a dafa wannan wake fari da wannan rubutu
sai a ci wannan wake
Kullum haka za'ayi aikin na tsawon kwanaki 3 ko 7,
ana maimaitawa kullum.
Ana yin haka da fatan Allah ya saka albarka cikin wannan aiki 💗
Asararu Zallah foundation
08109934185

Comments
Post a Comment