Posts

Showing posts with the label kariya daga sihiri

SIRRIN KARYA JIFA DA SIHIRI MAI KARFI

Image
  SIRRIN KARYA JIFA DA SIHIRI MAI KARFI Assalamu alaikum jama'a ina yiwa kowa fatan alkairi fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya  Ga wani faida mai ƙarfin gaske wanda insha Allahu zakuji daɗinshi Duk wanda yake fama da matsalar jifa ko jinnu ko kuma wani in yazo wurinka da irin wannan matsalar Abinda zaka fara yi shine ka nemi farin takarda ka rubuta wannan hatimin Yadda kake ganinshi sai ka rubuta sunanka a tsakiyar hatimin ko sunan wanda ya kawo maka aikin karya jifa Bayan ka gama sai ka naɗe ka ɗaura akan charbinka kayi wuridin wannan ayar وقدمنا الى ما عملوا من عمل فجعلنه هباء منثورا (WAQADIMNA ILA MA AMILU MIN AMALIN FAJA'AL NAHU HABA'AN MANSURA) Ƙafa 12,000 kullum (dubu goma sha biyu) to insha Allahu idan akayi haka na tsawon sati biyu ko sati ɗaya komai zai karye Ga Hatimin nan: Asararu Zallah Foundation 08109934185

SIRRIN WARWARE KO WANNE IRIN ASIRI A JIKIN MUTUM

Image
SIRRIN WARWARE KO WANNE IRIN ASIRI A JIKIN MUTUM Wannan sirrin yana daya daga cikin manya manyan sirruka da muka jima muna bawa Jama'a shi kuma Jama'a dayawa suna amfana daga sirrin inda mutane dayawa suke mana godiya akan sirrukan indai SIRRIN WARWARE KO WANNE IRIN ASIRI A JIKIN MUTUM ne to tabbas ku jarrabashi zaku ga faidar shi. Zakuga cewa lokuta da dama mutane suna fama da matsaloli musamman a jifa a jikinsu kuma sun kasa gano hanyar da zasu bi domin magance wannan matsalar saboda halin rayuwa da ake ciki in sha Allahu ga wannan sirrin sai a jarraba. Yadda ake aikin shine ana rubuta Suratul Yasin kafa 7 a cikin kwanaki 14 na ƙarshen wata, sai a wanke, bayan nan sai a Nemo kan gatari, ruwan gatari kenan da aka riga aka yi amfani da ita, kada ta zama sabuwa, mafi so ta kasance tsohuwa gaskiya. Sai a zuba wannan rubutun a sabon tukunyar kasa, shi kuma kan gatarin a daura akan wuta har sai ya yi ja yayi zafi sosai, sa’annan sai ka saka shi cikin wannan rubutun na cikin tukunya...