Posts

Showing posts with the label kariya da arziki

Sirrin Samun Dukiya Da Rufin Asiri - Asararu Zallah

Image
  Sirrin Samun Dukiya Da Rufin Asiri - Asararu Zallah Ana samun ganyen gwandar daji guda 666 ko wanne Ana rubuta masa Wannan Tauraron ramlin mai suna Isqafi kafa 666. Sai a wanke wannan zanen, sannan a yi wanka da shi tsawon kwanaki 3 idan namiji ne, ko kwanaki 4 idan mace ce. A lokacin da ake yin wankan, ana hawa wani abu mai ɗan tsawo kamar dutsen ƙarami, ko kujerar da ke sama, ana yin hakan don nufin cewa mutum zai hau matsayi mai girma ko samun buɗewa. Wannan sirrin yanada girma sosai kada ayi wasa dashi, dan nasameshine daga daya daga cikin malaman kasar Senegal wanda yasha bani sirruka masu karfin gaske kuma tabbas idan na jarraba su ina ganin biyan bukata dai dai gwargwado Alhamdulillah. Saboda haka kuma ku rike shi zaku ga amfanun shi insha Allahu rabbi. Asararu Zallah foundation  08109934185

Dafa'i Da Jalabi Mai Karfin Gaske

Image
  Dafa'i Da Jalabi Mai Karfin Gaske Yan uwa ahlullahi ina yiwa kowa fatan Alkairi da kuma fatan samun nasara a duk in muke. Sirrin: Dafa'i Da Jalabi Mai Karfin Gaske sirrine mai girma kuma yana daya daga cikin sirrukan da muke aiki dasu. Allahumma salli ala sayyadina Muhammadu Alfatihi lima ugliqa wal katimi lima sabaqa nasiril haqqi bil haqq wal hadi ila siradikal mustaqim wa'ala ahlihi haqqa qadrihi wa miqidarihil azim. Wannan sirrin sirrine na dafa'i kuma jalabi kuma ibɗali saboda hatimine na Alqur'ani mai girma kuma JAMIUL KULLI A rubuta shi asha a shafe jiki na tsawon kwana 7, son samu ace kullum ƙafa 7 kai ko ƙafa ɗaya ne yayi, insha Allahu za'a dace. Duk mai matsalar rashin jalabi zai iya jarraba shi, mai matsala rashin dafa'i ma zai iya aikatashi duk matsalar da kake dashi xaka iya aiki dashi kuma za'a ga biyan bukata insha Allahu. Ga hatimin nan: Asararu Zallah foundation 08109934185