Posts

Showing posts from May, 2025

Wuridin Mallakar Miji Mai Karfi Cikin Gaggawa

Image
Jama'a sun sha tambayar mu sirruka musamman akan mallaka da kuma jawo hankalin masoyi, wanda da yawan mutane sun sha jarraba wasu ayyukan da dama, zaka ji wasu ma suna cewa sun jarraba, sun jarraba amma har yanzu basu dace ba, abunda nakeso mutane su gane shine, idan akace Sirri kowanne iri ne yana bukatar wasu abubuwa kamar guda uku zuwa hudu wanda Sune zasu saka wannan sirrin ya tashi, gasu kamar haka: Yakini (Yin Imani Da Zuciya Daya) Wannan shine mataki na farko mafi karfi da yake sanya idan mutum yayi sirri kaga sirrin ya tashi, ba dan komai ba sai fadin Allah madaukakin sarki da yake cewa yana aiki da zuciya ne. Saboda haka zuciya itace abu na farko mafi mahimmanci da zaka tsarkake matsawar kanason duk aikin da kayi ya tashi, in kuma bakayi haka ba, babu lallai kayi aiki kaga ya tashi domin zuciya shine sada ka tsakanin ka da Ubangijin ka, saboda haka duk sanda aka baka wani sirri ko kake jarraba wani sirri to kayi shi da zuciya daya, ka kuma saka a ranka cewa bukatar ka ta b...