SIRRI AKAN KOWACE IRIN DAMUWA KO BUKATA

 


SIRRI AKAN KOWACE IRIN DAMUWA KO BUƘATA

‎Akoda yaushe ba'a taɓa raba mutum da damuwa in ma dai na kuɗi ko lafiya ko na halin zamantakewar rayuwa kowa da irin yadda Allah yake jarraba shi daga cikin Nau'o'i na damuwa kuma akoda yaushe ana fafutuka ne wajen ganin an samu waraka daga wannan damuwa muna fata Allah ya cigaba da yayemana damuwarmu baki ɗaya.

‎To kamar yadda muka faɗa in har kasan kana cikin wata damuwa kowacce iri ce ban rage maka ko guda ba kuma kake da burin ganin Allah ya ɗauke maka ita to ga wannan sirri ka jarraba shi ni dai fatana duk wanda yaga wannan sirri yayi ƙoƙarin yi don Allah don Annabi Muhammadu s.a.w wallahi wallahi babu kaffara acikin wannan rantsuwa in har Allah yabaka damar aiwatar da wannan to zaka samu kuɓuta daga cikin duk wata matsala ko damuwa sannan buƙatarka kowace iri ce Allah zai biya maka Insha'allahu.

‎Ga yadda zaka yi:

‎Zaka yi nafila raka'a huɗu kowacce raka'a Fatiha ɗaya Inna'anzalnahu ƙafa huɗu duk raka'a biyu kayi sallama sannan akowane canji acikin raka'o'i huɗu da zakayi zaka biya wannan sirri ƙafa Arba'in da ɗaya hakanan bayan sallama zakayi sujjada na musamman ka biya wannan sirri shima dai ƙafa Arba'in da ɗaya ka roƙi Allah wallahi baka ɗagowa daga wannan sujjada fa ce Allah ya yayemaka damuwarka kuma ya biya maka buƙatunka.

‎Misalin kowane canji shine bayan ka gama karanta Inna'anzalnahu huɗu a tsaye to idan kayi ruku'u sai ka biya sirrin arba'in da ɗaya hakanan idan ka ɗago daga ruku'u ka biya sirrin arba'in da ɗaya hakanan idan kayi sujjada ka biya sirrin arba'in da ɗaya hakanan idan ka ɗago daga sujjada ka biya sirrin arba'in da ɗaya ka koma kayi sujjada shima ka biya sirrin arba'in da ɗaya hakanan idan ka ɗago daga sujjada na biyu kafin ka miƙe tsaye ka biya sirrin arba'in da ɗaya sai ka miƙe ka kawo wata raka'an kamar haka to kuma haka zaka yi har raka'a huɗu.

‎Ga sirrin da zaka biya:

‎لا إله إلا أنت سبحانك إني كنت من الظالمين

‎Laa ilaaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzaalimiin.

‎Allah ya baku ikon aiwatarwa Albarkacin Annabi Muhammadu s.a.w kamar kullum hadiyyan wannan sirri shine kuyi salati ga Annabi sannan kuyi Sharing na wannan posting zuwa ga masoya Annabi Muhammadu domin su amfana domin mu muna baku ne domin mu amfanar daku Allah ya sanya mudace duniya da lahira.


Asararu Zallah foundation 

08109934185

Comments

Popular posts from this blog

Sirrin Warware Duk Wani Kulli Da Nahisantakar Tauraro

Wuridin Mallakar Miji Mai Karfi

Sirrin Maganin Mayu Sadidan, Mai Tarwatsa Mayu