Sirrin Biyan Bashi Nan Take Mujarrabun
Sirrin Biyan Bashi Nan Take Mujarrabun.
Ga waɗanda suke bashi yai musu yawa kuma ba sa iya biya, ma'ana Allah bai hore musu abunda zasu biya dashi ba to ga wani sirri da zasu iya jarrabawa insha Allahu za'a samu biyan bukata cikin kankanin lokaci.
Ana rubuta wannan tauraron na ramli wanda ake kiranshi da naqiyyatul khaddi, shine tauraron gidan 14 a taurarin ramli, wannan tauraron ana rubutashi ne kafa 945.
Ma'ana ana samun babban Allo sai a dinga rubuta wannan shakalin ai ta rubuta shi har sai an tabbata ya kai kafa 945 babu ragi ba kari, a kula idan aka rage aiki bazai yuwu ba, hakama idan aka kara aiki bazai yuwu ba saboda haka ayi rubutun da taka tsantan ko mai ya futo dai dai saboda samun cikar biyan bukata.
Yadda ake amfani da shi:
Wannan rubutun idan ka gama shi zaka samu ruwa mai tsarki mai tsabta sai ka wanke shi bayan ka wanke shi sai kake shafa shi a jikin ka safe da yamma na tsawon kwanaki 9, tare da yin addu’o’in bukatunka, ma'ana addu'oi akan Allah ya baka ikon biyan wannan bashin cikin gaggawa, kuma ka tsarkake zuciyar ka yayin yin wannan addu'ar.
In sha Allah, za ka sami agaji daga inda ba ka zata ba wajen biyan bashin ka. Wannan sirrin “Kun fayakun” har ma idan kana tattara ƙasa ne, Allah zai ba ka mafita.
Da zarar ka ga an amsa maka, ka yi sadaka da madarar saniya sabuwa ga marasa karfi a gaban masallaci.
Allah Ya sa albarka, Ya karɓi addu’a.
Ga hoton tauraron:
Asararu Zallah foundation
08109934185


Comments
Post a Comment