Sirrin Bude Manyan Alheri: Salatin 1813 ga Kashifu al-Ghumma
Sirrin Bude Manyan Alheri: Salatin 1813 ga Kashifu al-Ghumma
📖 Bayani Mai zurfi Ma’anar “كَاشِفُ الْغُمَّةِ”
“Kashif al-Ghumma” (كَاشِفُ الْغُمَّةِ) na nufin Mai cire damuwa ko Mai warware ƙunci (wato Allah ne wanda yake kawar da damuwa).
Salatin “اللهم صل على كاشف الغمة” yana nufin “Ya Allah, ka yi salati (fatan rahama da salama) ga Mai Cire Damuwa” — wato an nufi Annabi Muhammad ﷺ a matsayin wanda addu’o’insa, albarkarsa, zasu taimaka wajen sassauta wahala da damuwa.
Wurin wannan salati a cikin ibada:
Ana cewa a karanta wannan salati kafa 1813 da dare, bayan sallar Tahajjud (wato bayan farkawa da dare don yin ibada) ba tahujjud na ramadan ba, ana nufin sallar nafila da akeyi da daddare.
Ana maimaita wannan salati tsawon kwanaki 21, Wannan hanya ana ɗaukar ta a matsayin wata ibada mai karfi da ake sa ran Allah zai buɗe babban alheri, sassauta damuwa, ya kawo sauƙi da ƙarin rahama ga mai yin ta da zuciya da tawakkali.
Sharhin Ilmi da hankali.
Kamar kowace addu’a ko salati, tsoron Allah, niyya mai kyau, da imani ne ke zama ginshiƙi — ba laifi ba ne mutum ya nemi albarka da sauƙi daga Allah, ka tuna Allah na cewa: Allah ne mafi iko, kome yana hannunsa. Salati da addu’a suna taimako ne idan mutum yana haɗawa da aiki nagari, tawakkali, ɗawainiya da tsoron Allah. Fa’idodin da ake fata Sassauta damuwa, ƙarin nutsuwa da ƙarfin zuciya Buɗe manyan alherai da rahama daga Allah Neman tsaro daga sharrin zuciya da matsaloli Kara kusanci da Manzon Allah ﷺ da samun fadakarwa cikin ibada

Comments
Post a Comment