Posts

Sirrin Mallaka Maza Da Mata

Image
  Sirrin Mallaka Maza Da Mata Wannan Sirrin Mujarrabun ne ga maza da mata masu neman Mallaka ga ko wanene walau miji da mata ko mai gida da yaron gida ko dan uwa da yar uwa ko saurayi da budurwa kowa zai iya jarraba wannan sirrin, shiyasa muke kiranshi da Sirrin Mallaka Maza Da Mata, zakuji dadin shi sosai insha Allahu, ku jarrabashi zaku bamu labarinshi domin sirrine da muka tabbatar da cewa bazai Baku kunya ba. Yadda Ake Aikata Sirrin Ana rubuta wannan akan Allon karfe ko akan takarda ko akan yashi sannan a saka sunan wanda ake so a tsakiyar hatimin, idan a takarda aka rubuta sai a daura akan carbi, bayan an shirya sai a shafa turare mai kamshi, a zauna ayi wurudin tabbat yada kafa 449 sannan sai ayi wuridin Ya wadudu kafa 5395, bayan an gama sai kayi wannan azimar "Allahumma Aj'al Muhabbatiy fi qalbi (Sai ka fadi sunan ta ko sunan shi) bihaqqi Ahamun Saqakun Hala'un Yassun wa bi hakki bismillahi rahmani rahim" kafa 7, kullum haka zakayi na tsawon kwana bakwai, aiki...

JALABI DA DAFA'I NA YANKAN SHAKKU

Image
  JALABI DA DAFA'I NA YANKAN SHAKKU Ina yiwa al'ummar wannan gidan fatan alkairi fatan kowa zai sha ruwa lafiya  Yau ma muna tafe da wannan gagarumin sirrin mai suna JALABI DA DAFA'I NA YANKAN SHAKKU , wanda nayi duba da kasancewarmu a wata mai falala da albarka muyi kokari mu amfana albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Wannan aikin jalabine (buɗi mai girma) kuma Dafa'i ne (kariya mai girma) wanda Allah ya bashi ikon aikatawa to tabbas zai yi godiya Yadda ake aikin shine ana shiga halwa na tsawon adadin kwanakin da zai isheka ka kammala wannan aikin  Ana karanta wannan salatin ƙafa DUBU ƊARI DA ASHIRIN 120,00 Idan an shiga Wannan halwar sai an gama za'a fito zakaga abun al'ajabi kuma ba'a cin abin haramun lokacin da ake halwar duk abinci ko abin sha da za'a ci a tabbatar na halal ne wallahi jalabi ne kuma Dafa'i na yankan shakku har mutane zasu fara tinanin mutum ya shiga ƙungiyar asiri ga salatin nan ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDNA MUHAMMADIN SA...

Dafa'i Da Kariya Daga Mugaye

Image
  Dafa'i Da Kariya Daga Mugaye Wannan sirrin wallahi billahi tallahi, duk wanda yake yawan karanta shi to duk sharrin mai sharri sai dai yayi hakuri saboda daki bari ne, zaku ke yawan jinshi a wakokin sirrin fatahi ko Ahmad Abdallah saifi ne mai karfi ana karanta shi kafa 77 wallahi sai ka ga canji kai da kanka Gashi nan: Ya sad'watullahi hillu aqadu ma rabbadu. Wa shattati shamla aqwani bina ahtaladu. Allahu Akbar Saifullahi fa'di-uhum. fakullama  qad alau fi ra'ihim habidu. Indai kuka dage da karanta wannan baitin wallahi tallahi mutum ko aljanine shi kafi karfin sa, zaka samu cikakkiyar dafa'i zaka samu cikakkiyar kariya mara misaltuwa zaka tumbatsa duk wanda ya nemeka da sharri sai ya gane shayi ruwane ko wanene shi. Kada ku manta akwai littafin mu wanda muka wallafa shi yana dauke da sirruka sama da 500 kuma sirrukan ciki mujarrabun ne wayanda aka jarraba ne kamun aka kawo muku shi, sirrukan duka da hausa aka rubuta su, ga masu bukata zasu iya mana magana a Wha...

SIRRIN DAFA'I DAKE RUSA MAKIYA DA DUK SHARRIN SU

Image
  SIRRIN DAFA'I DAKE RUSA MAKIYA DA DUK SHARRIN SU Wannan sirrin yana daya daga cikin manyan sirrukan da aka jarraba su daga cikin dayawa daga cikin almajiran ahlul sirri Kuma tabbas an samu biyan bukata Kuma tabbas sirrin mujarrabun, hatimin yana dai dai da hizbul saifi. Akwai wani dan uwa da muka taba bashi sirrin, Wanda shi Allah ya jarrabeshi da rashin samun bacci saboda yawan razana da yakeyi duk Sanda ya kwanta bacci sanadiyyar makiya sun saka shi a gaba sosai, Amma cikin ikon Allah da muka bashi sirrin nan ya ga ikon Allah akanshi. Shiyasa muke son Kuma ku rabauta da wannan sirrin. Yadda ake aiki dashi: Ana rubuta hatimin kafa 40 ana sha Kuma ayi wanka dashi na tsawon kwana 3 safe da yamma, Amma ana samun tsohon karfe a sakashi a wuta sai yayi ja sai a saka shi a cikin rubutun kamun ake sha Kuma a yi wanka da ragowar. Wannan sirrin dai mun jarraba shi Kuma muna masu tabbatar muku da ingamcin sa, sannan insha Allahu duk wani abu da zaku gani acikin wannan website din zakuji d...

JALABI DAGA MAULAN MU SHEHU IBRAHIM INYASS

Image
  JALABI DAGA MAULAN MU SHEHU IBRAHIM INYASS Wannan jalabin ya samu ne daga hannun maulanmu shehu Ibrahim inyass r.t.a, wanda ya shiga hannuwan muridansa da yawa shiya sa mu ka kirashi da JALABI DAGA MAULAN MU SHEHU IBRAHIM INYASS. Sirrin mu mujarrabun ne a wajen mu saboda mun jarraba shi ba sau daya ba, ba sau biyu ba, muddin mutum yana yawan istigfari da wasu auradan sannan yana kamewa daga aikata mummunar aiyuka na zunubi duk da (ان النفس لامارة بالسوء الا ما رحم ربى ان ربى غفور رحيم) To sai dai yawan neman gafarar ubangiji da kuma neman yardarsa yana taimakawa mutum wajen samun natija da biyan bukata kad'an. Bamu san adadin mutanen da muka taimakawa haka bamu san adadin wayanda muka batawa ba, mudai fatan mu shine a koda yaushe muga gusto fuskokin ku cikin farin ciki da nishadi, mu almajiran shehu ahmadu tijjani yan Faidar shehu Ibrahim inyas sannan dagirawa masu aqidar Nufan Allah da halarar shi. Saboda haka ga wannan jalabin sai a jarraba. Yadda ake aikin: Ana karanta LAILAHA...

MALLAKAR DUK WANDA AKE SO KO WAYE SHI

Image
  MALLAKAR DUK WANDA AKE SO KO WAYE SHI Wannan sirrin muna amfani dashi sosai kuma muna ganin ijabarsa, akwai wayanda suna aikata sirri amma basa ganin ijabarshi na farko su binciki kansu na biyu su yawaita yin istigfari da salatin annabi ace a rana kanayin istigfari dubu 41 ko 70 salatin annabi dubu 10 ko 41 insha Allahu in dai ka yawaita yin hakam kuma kabi lokacin da ya dace da kowanne aiki zaka ga budi da biyan bukata sannan zaka samu cikakken ijaba, sirrin MALLAKAR DUK WANDA AKE SO KO WAYE SHI insha Allahu. Wannan sirrin ko gobna kayi wa zaka samu cikakken soyayyar shi kuma duk bukatar da kake nema na gidan duniyar nan a wajen shi zai biya maka in har yana dashi, saboda haka aji tsoron Allah, sirrine daga hannun maulanmu shehu ahmadu tijjani kada ayi wasa dashi. Yadda ake aiki da wannan sirri: Ana rubuta wannan hatimin mai rijiya akan farin takarda sai a saka sunan wanda akeso a mallaka a tsakiyar hatimin inda babu komai sai a rataye a wuya ko akan charbi, shi Kuma dayan hatim...

SIRRIN WARWARE ASIRI MAI KARFIN GASKE

Image
  SIRRIN WARWARE ASIRI MAI KARFIN GASKE. Assalamu alaikum yan uwana musulmai masu daraja, masoya Manzon Allah masoya maulanmu ahmadu tijjani yan Tijjaniyya da wayanda ba yan Tijjaniyya ba, zakirai da mahaddata Alqur'ani ina yiwa kowa fatan Alkairi, muna kaunar ku Allah ya barmu tare ameen! Wannan sirrin da kuke gani sirri ne na warware asiri shine muke kira da "Ibdalil Sihir" ko kuma SIRRIN WARWARE ASIRI MAI KARFIN GASKE, sirrine wanda ya shahara wanda dayawa daga cikin malamai ke amfani dashi domin warware duk wani nau'in asiri dake jikin mutum insha Allahu zaku amfana kwarai da gaske da wannan sirrin kuma duk wani almajiri mai aikin makaranta zai amfanu dashi sosai, mun yiwa kowa izini kamar yadda muma akayi mana izinin shi. Yadda ake aiki dashi shine, ana samun farar takarda marar zane sai a rubuta wannan rubutun na jikin takardar sai kuma hatimin a kasan rubutun bayan an gama sai a nade layar a rataya a jiki ko a ratayawa mara lafiyar sannan kullum za'a ke rub...