MALLAKAR DUK WANDA AKE SO KO WAYE SHI

 

MALLAKAR DUK WANDA AKE SO KO WAYE SHI

Wannan sirrin muna amfani dashi sosai kuma muna ganin ijabarsa, akwai wayanda suna aikata sirri amma basa ganin ijabarshi na farko su binciki kansu na biyu su yawaita yin istigfari da salatin annabi ace a rana kanayin istigfari dubu 41 ko 70 salatin annabi dubu 10 ko 41 insha Allahu in dai ka yawaita yin hakam kuma kabi lokacin da ya dace da kowanne aiki zaka ga budi da biyan bukata sannan zaka samu cikakken ijaba, sirrin MALLAKAR DUK WANDA AKE SO KO WAYE SHI insha Allahu.

Wannan sirrin ko gobna kayi wa zaka samu cikakken soyayyar shi kuma duk bukatar da kake nema na gidan duniyar nan a wajen shi zai biya maka in har yana dashi, saboda haka aji tsoron Allah, sirrine daga hannun maulanmu shehu ahmadu tijjani kada ayi wasa dashi.

Yadda ake aiki da wannan sirri:

Ana rubuta wannan hatimin mai rijiya akan farin takarda sai a saka sunan wanda akeso a mallaka a tsakiyar hatimin inda babu komai sai a rataye a wuya ko akan charbi, shi Kuma dayan hatimin murabba'i za'a rubutashi ne a allo kafa 9 tareda alamnashrah sai a wanke shi asha kullum, 

Sai a zauna ayi wuridin:

YA MUSAKKIRU SAKKIRLI (SAI KA FADI SUNANSHI) kafa 313

YA HABIBU kafa 2000

FATIHATUL KITAB kafa 99

ARSADAN MAKSUHIN ALQABIDU HATARANZAGIYU kafa 99

YA SHAIJAKAZISHUN kafa 2000

YA SHAIJAKAZIY SHAIJAKAZISHUN kafa 700

YA AMJILAHABLAMALIHUDIR 288


Aikin ayishi na tsawon kwana 9 ko 7 ko 21 

Wannan sirrin fa ba karamin sirri bane a kiyaye

Ga hatimin nan:




#kundinsirri

Comments

Popular posts from this blog

Sirrin Warware Duk Wani Kulli Da Nahisantakar Tauraro

Wuridin Mallakar Miji Mai Karfi

Sirrin Maganin Mayu Sadidan, Mai Tarwatsa Mayu