SIRRIN DAFA'I DAKE RUSA MAKIYA DA DUK SHARRIN SU

 


SIRRIN DAFA'I DAKE RUSA MAKIYA DA DUK SHARRIN SU

Wannan sirrin yana daya daga cikin manyan sirrukan da aka jarraba su daga cikin dayawa daga cikin almajiran ahlul sirri Kuma tabbas an samu biyan bukata Kuma tabbas sirrin mujarrabun, hatimin yana dai dai da hizbul saifi.


Akwai wani dan uwa da muka taba bashi sirrin, Wanda shi Allah ya jarrabeshi da rashin samun bacci saboda yawan razana da yakeyi duk Sanda ya kwanta bacci sanadiyyar makiya sun saka shi a gaba sosai, Amma cikin ikon Allah da muka bashi sirrin nan ya ga ikon Allah akanshi.


Shiyasa muke son Kuma ku rabauta da wannan sirrin.


Yadda ake aiki dashi:


Ana rubuta hatimin kafa 40 ana sha Kuma ayi wanka dashi na tsawon kwana 3 safe da yamma, Amma ana samun tsohon karfe a sakashi a wuta sai yayi ja sai a saka shi a cikin rubutun kamun ake sha Kuma a yi wanka da ragowar.

Wannan sirrin dai mun jarraba shi Kuma muna masu tabbatar muku da ingamcin sa, sannan insha Allahu duk wani abu da zaku gani acikin wannan website din zakuji dadin shi domin duk abunda zamu kawo shi nan mujarrabun ne sai mun jarraba shi muke kawo shi domin gudun kada mu kawo muku abunda zaku sha wahalan aikata shi.

Domin dayawan mutane suna kawo sirruka birjib wanda in mutum ya jarrabashi sai kaga bai samu biyan bukatar da yake nema ba wanda hakan yakan jefa mutane da dama cikin rudanin shin ko dai basuda ijaba ne ko kuma dai akwai wata matsalar ne, wanda dayawa daga sirrikan ne.


Allah ya bada ijaba ameen


#asararuzallahfoundation

08109934185

Comments

Popular posts from this blog

Sirrin Warware Duk Wani Kulli Da Nahisantakar Tauraro

Wuridin Mallakar Miji Mai Karfi

Sirrin Maganin Mayu Sadidan, Mai Tarwatsa Mayu