SIRRIN SAMUN BUDI DA RUFIN ASIRI
SIRRIN SAMUN BUDI DA RUFIN ASIRI
Assalamu Alaikum Jama'a kuyi hakuri zakuga ba kullum muke kawo muku sirruka ba saboda shaanin rayuwa kuma bamaso mu kawo muku sirri marasa inganci munfi son mu kawo sirrin da muka jarraba shi domin kuma ku samu dace akai kamar yadda sauran yan uwa almajirai sukayi amfani dashi suka ga abun mamaki.
A kullum muna kara tunatar daku cewa Allah shiyace mu rokeshi zai amsa mana saboda haka musaka a rammu cewa Allah ne zai biya mana bukatun mu ba wani ba, kuma duk girman sirri idan babu yardar Allah aciki to babu wata cikar muradi acikin ta, yardar Allah shine komai.
Wannan sirrin in dai kayi shi zakaga abun mamaki wallahil azim, wayanda suka jarrabashi sunga budi da kuma rufin asiri, wasu sun samu mota, wasu gida wasu Kuma yan chanjin da zasuyi hidima dasu sannan a sani ba tasrifi bane yawwa wannan jalabi ne na gaske.
Yadda Ake Aikata wannan sirrin:
Da farko ana Rubuta wannan hatimin a farar takarda ko akan yashi ka ajje a gabaka ko kuma ka zanashi a farar takarda mara zane, sai kayi laya dashi ka daura shi akan charbin ka, bayan kayi haka ka tattaro duk nutsuwarka da kuma bukatunka ka nufi ubangiji dashi, ka fara wuridin وجعلت له مالا ممدودا (Wa ja'altu Lahu Malan Mamduda) kafa 3,538,647 (Milyan uku da dubu dari biyar da dubu talatin da takwas da dari shida da arba'in da bakwai) ba lokaci daya ake gama aikin ba zaka iya daukan adadi ko kuma kake rubuta duk adadin da kayi har sai ka cike wannan adadin sannan lokacin da aka fara wannan aikin a kiyaye maganganun batsa, ko kallon abun batsa ko kuma yawan zagi ko yawan surutu a kame kai a kasance ana zama cikin tsarki, a kiyaye shiga tiktok ko wasu wuraren da za'a iya ganin abubuwan batsa, wallahi thumma tallahi wanda yayi aikin nan sai yayi mamakin jalabi da budi daga wajen ubangiji wallahi har mota ko gida sai ya mallaka.
Wannan sirrin tabbas mujarrabun ne mun jarraba shi Kuma munga Fa'idarshi kada kuyi kokonto akan shi domin sirri ne mai karfin gaske in dai budi da kuma samun biyan bukata a wajen ubangiji, na tabbata babu wanda zai jarraba wannan sirrin ba tareda yayi mana godiya ba sirri ne mujarrabun na gasken gaske Jama'a dayawa sunji dadin shi.
Kuma kada ku manta ku saka mu acikin addu'oin ku da kuma duk wani sha'aninku yan uwa na. Ga hatimin nan a kasa.
Asararu zallah foundation
08109934185


Comments
Post a Comment