Wannan jalabine mai kyau, kuma da yawa daga cikin yan uwan mu almajirai sunyi aiki dashi kuma sunji dadin shi, ku sani a wannan rayuwar yanada kyau ace mutum yana da jalabi mai karfi Shiyasa muka yi kokarin dan gani mun kawo muku wannan sirrin mai albarka domin taimakawa almajirai yan uwa masoya Annabi YADDA AKE AIKI DASHI Ana rubuta suratu Dahe Amma kowacce Aya za'a saka wannan Ayar ان هذا لرزقنا ما له من نفاد ƙafa uku a wanke a sha kwana 7 amma ranar Alhamis ake fara aikin, ga wanda bazasu iya rubutun ba ga sauƙi, in suka rubuta wannan hatimin duk abu ɗaya ne a rubuta shi ƙafa uku a sha a roki Allah kwana 7