SIRRIN SAMUN MANYAN KUDADE
Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu, yan uwana almajirai masu albarka ina yiwa kowa fatan Alkairi fatan kuna cikin koshin lafiya amin.
Bayan gaisuwa ina kara mika godiyata gareku ina ganin addu'oin ku da fatan alkairi tabbas ina jin dadi kuma ina alfahari daku a koda yaushe, hakan ne ma yake kara bani kwarin gwiwar ganin na taimakawa sauran yan uwana Almajirai da wasu hanyoyin da ubangiji ya huwace mun.
Kamar yadda kuka sani yanada kyau ace mutum musamman musulmi kuma almajiri yanada wayan nan abubuwan guda biyu
1 jalabi
2 dafa'i
Duk fadi tashin ka a rayuwa kada ka rasa su, kasancewarsu tare dakai shi zai sanya abubuwan ka suke tafiya maka yadda kake so kuma zakaji dadin rayuwarka ba tareda kayi rayuwa cikin kunci ba
Saboda haka yasa zan baku wannan sirrin wanda yake Mujarrabun a wurin mu mun jarrabashi ba sau daya ba ba kuma sau biyu duk sanda muka ga mun dan shiga cikin wani hali to wannan sirrin muke aikatawa sai kaga Allah ya kawo mafita cikin gaggawa, kasani Allah ne yake komai Addu'a kuma tokobi ne kuma kofa dake sadaka Da ubangijin ka, sanin kowa ne ubangiji maji rokon bayi ne kuma mai amsa musu a duk sanda suka fada cikin wani yanayi.
Ga duk wanda zai yi amfani da wannan sirrin to ya yi kokari ya tsarkake zuciyarshi sannan ya tsarkake niya da jikinshi akwai wayanda ma na sani duk sanda zasuyi amfani da wannan sirrin sai sunyi azumi saboda yadda suke ganin girman sirrin a wajen su, amma fa ba dole bane mutum sai yayi azumi a fahimta
YADDA AKE AIKIN
Ranar Alhamis Karfe 6:30 na safe ka tsabtace jikinka da inda zakayi aikin da kuma tufafin ka, ka samu turaren ka mai kamshi dan duri sai ka kebe a wurin da babu surutu sosai sai kayi wuridin;
1 istigfari kafa 313
2 salatin annabi 100
3 lailaha illallah 100
Sai kuma kayi wuridin wannan ayar
ومن يتق الله يجعل له مخرجا ويرزقه من حيث لا يحتسب ومن يتوكل على الله فهو حسبه ان الله بلغ امره قد جعل الله لكل شيء قدرا
Kafa 313
Sai wannan ayar;
واذا راوا تجرة او لهوا انفضوا اليها وتركوك قائما قل ما عند الله خير من اللهو ومن التجرة والله خير الرزقين
Kafa 313
Sai kuma wannan ayar;
زين للناس حب الشهوت من النساء والبنين والقنطير المقنطرة من الذهب والفضة والخيل المسومة والانعم والحرث ذلك متع الحيوة الدنيا والله عنده حسن المءاب
Kafa 313
Bayan ka gama sai ka karanta ayatul kursiyu kafa 61
Ka roki Allah bukatar ka, amma aikin ana yinshi ne na tsawon kwana 3 ko 7
Sannan za'a iya yin shi karfe 1:30 na rana ko 8:30 na dare ko 3:30 na dare
Allah ya sa mu dace ameen thumma ameen
جزاك الله خيرا كثيرا وشكرا عليك يا سيدي يا شيخ الكبير
ReplyDelete