Sirrin Fatiha Mai Karfin Gaske
Sirrin Fatiha Mai Karfin Gaske
Wannan ismin yana daya daga cikin manyan ismi wanda aka cireshi daga sirrin fatiha mai karfin gaske, Wannan sirrin manyan malamai sunyi ittifaqin cewa yana daya daga cikin asararu masu saurin ijaba wannan dalilin ne ma ya saka dayawa daga cikin su basa yarda su bawa wani sirrin sai in ya zama daya daga cikin ahalin su ko kuma dangin su, alhamdulillah yau zan baku wannan sirrin na fatiha fisabilillah da fatan sauran yan uwa musulmai zasu amfana dashi.
Yadda ake aikin shine:
Ranar alhamis, karfe 6:30 na safe ko 1:30 na rana ko 8:30 na bayan sallar isha, ko kuma 3:30 na daf sallar asubahi, Ana samun waje mai tsarki da kaya mai tsarki a samu turaren kamfani a shafa a jiki a zauna ayi niyan abunda ake bukata a fara da wuridin istigfari kafa 100, salatin annabi kafa 100, lailaha illallah kafa 100, sai kuma a soma wuridin wannan ismin
ARSA'DAN MAKSUHU ALQABIDU HATARANZAGIYU kafa 3,605 bayan an gama sai ayi fatiha kafa 41 kullum har tsawon kwana 7 insha Allahu wannan aikin mujarrabun ne kuma yanada kyau sosai kada ayi wasa dashi.
Comments
Post a Comment